29 Yuni 2020 - 07:03
Chadi : An Yi Wa Shugaba Deby, Karin Girma Zuwa Marshal

Majalisar dokokin Chadi, ta amince da kudirin yi wa shugaban kasar Idriss Deby Itmo, karin girma zuwa matsayin Marshal.

(ABNA24.com)  Majalisar dokokin Chadi, ta amince da kudirin yi wa shugaban kasar Idriss Deby Itmo, karin girma zuwa matsayin Marshal.

Shugaban majalisar dokokin kasar, Haroun Kabadi, ya ce shugaban kasar ya cencenci wannan girmamawa, saboda a jan kokarin da ya yi a ciki da wajen kasar.

Dan shekara 68, Janar Idriss Deby, ya kwashe shekaru 30 yana shugaban kasar ta Chadi.

A watan Maris, idan ana tune, an ga shugaban kasar sanye da kakin soji yana jagorantar ayyukan yaki da kungiyar boko haram a kewayen tafkin Chadi, har zuwa cikin wasu yankunan kasashen Najeriya, Nijar da Kamaru bayan wani mummunan hari da ya yi sanadin mutuwar sojojin kasarsa kimanin 100.

Saidai ‘yan majalisar dokokin kasar na bangaren adawa basu halarci zaman majalisar ba, wanda a yayinsa aka amince da yi wa shugaban kasar karin girma zuwa Marshal.


/129